An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wadanne dabi'u ne na Musulunci suka fi? sai ya ambaci dabi'u biyu: Na farko: Yawaita ciyar da abin ci ga talakawa, sadaka da kyauta da saukar bako da walima za su shiga ciki, falalar ciyarwa tana karfafa alokutan yunwa da tsadar farashi. na biyu: Yin sallama ga kowanne musulmi, ka san shi ko ba ka san shi ba.