Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitar da musulmi da yin sallama ga ɗan uwansa musulmi duk lokacin da ya haɗu da shi, koda sun kasance suna tafiya tare ne kuma wani abu mai rabawa ya raba su, kamar bishiya ko gini ko babban dutse, sannan ya haɗu da shi bayan nan to ya yi masa sallama karo na biyu.