Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana shiryarwa ga ladabin yin gaisuwar Musulunci tsakanin mutane "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarsa", Sai karami ya yi sallama ga babba, wanda ke kan abin hawa ga mai tafiya a kasa, mai tafiya a kasa ga wanda ke zaune, adadi kadan ga adadi mai yawa.