Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga farawa Yahudawa da Nasara da sallama koda sun kasance kafiran amana ne, ballantana wasunsu cikin kafirai, kuma tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mu idan mun haɗu da ɗayansu a wata hanya to mu buƙace shi zuwa mafi ƙuncin hanyar, to mumini shi ne wanda yake tafiya a tsakiyar hanya, wanda yake nesa (da hanya) shi ne kafiri, kuma musulmi ba ya kasancewa ƙasƙantacce da wani hali daga halaye.