explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana sashin hakkokin musulmi akan dan uwansa musulmi. Farkon wadannan hakkokin su ne maida sallama ga wanda ya yi maka sallama. Hakki na biyu: Gaida mara lafiya da ziyartarsa. Hakki na uku: Bin jana'iza daga gidansa zuwa wurin yin sallar, kuma zuwa makabarta har a binneta. Hakki an hudu: Amsa gayyata idan ya gayyace shi zuwa walimar angwanci da wanin hakan. Hakki na biyar: Gaida mai atishawa, shi ne ya ce masa idan ya godewa Allah: Allah ya yi maka rahama, sannana mai atishawar ya ce: Allah Ya shiryeku Ya gyara halayenku.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Girman musulunci a karfafa hakkoki tsakanin musulmai da karfafa 'yan uwantaka da soyayya a tsakaninsu.