Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi ya bada labari cewa da wani zai leka gidan wani ta bayan kofa ko ta saman katanga ko makamanci hakan, sai ya jefe shi da dutse ko ya soke shi da wani karfe a ido, to ba wani abu na zunubi ko na kisasi; Don kuwa shi ya janyowa kansa.