explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya yi hani game da ƙauracewar musulmi ga ɗan uwansa musulmi sama da dare uku, kowane ɗaya daga cikinsu zai haɗu da ɗayan, amma ba zai yi masa sallama ba, kuma ba zai yi masa magana ba. Mafificin waɗannan masu husumar biyun shi ne wanda zai yi ƙoƙarin gusar da ƙauracewar, kuma ya fara yin sallama, abin nufi da ƙauracewa a nan shi ne na son rai, amma kauracewa saboda haƙƙin Allah - Maɗaukakin sarki - kamar ƙauracewa masu saɓo da 'yan bidi'a da mugayen abokai, to, wannan ba a iyakanceshi da wani lokaci, kawai ya na rataya ne da maslaha a ƙauracewar, kuma yana gushewa da gushewarta.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Halaccin ƙauracewa na kwana uku, da ƙasa da hakan, don kula da ɗabi'un mutane, sai akayi afuwa a kan ƙauracewa a cikin kwana uku har wannan abin da ya bijirowar ya tafi.
  • Falalar sallama, kuma tana gusar da abin da ke cikin zukata, kuma alama ne a kan soyayya.
  • Kishin musulunci a kan 'yan uwantaka da sabo a tsakanin ma'abotansa.