explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fadakar da wanda zai yi hamma cewa buɗe bakinsa saboda kasala ce ko cika ko wanin haka; cewa ya ɗora hannunsa akan bakinsa sai ya rufeshi da shi; hakan domin Shaiɗan yana shiga cikinsa idan ya barshi a buɗe, to ɗora hannu yana zama mai hana shigarsa.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Idan mutum yana son yin hamma to ya wajaba a kansa ya rufe (bakinsa) daidai iko, cewa ya riƙe bakinsa, sai ya barshi a rufe ta inda ba zai buɗe ba, idan ba zai iya barin bakinsa a rufe ba to ya ɗora hannunsa akan bakinsa, sai ya rufe bakinsa da hannunsa.
  • Lazimtar ladubban Musulunci a dukkan halaye; domin cewa sune alamomi na cika da kuma ɗabi'u.
  • Kiyayewa daga dukkan mashigar Shaiɗan ga mutum.