Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa daga haƙƙin musulmi akan ɗan uwansa musulmi ɗabi'u shida ne: Na farko: Idan ya haɗu da shi ya yi masa sallama da faɗin: Assalamu alaikum, Wato: Aminci ya tabbata agare ku, shi kuma ya dawo da sallama da faɗinsa: Waalaikumus Salam, Wato: Aminci ya tabbata agare ku. Na biyu: Amsa gayyatarsa idan ya gayyace shi dan walima da makamancinta. Na uku: Yi masa nasiha idan ya nemeta, kada ka yi masa yaudara ko ka yi masa algus. Na huɗu: Idan ya yi atishawa sai ya ce: Godiya ta tabbata ga Allah, to ka gaishe shi da faɗin: (Yarhamukallah) Allah Ya yi maka rahama, shi kuma ya amsa yana mai cewa: Allah Ya shiryar da ku kuma ya gyara zuciyarku. Na biyar: Ya gaishe shi kuma ya ziyarceshi idan ya yi rashin lafiya. Na shida: Ya yi masa sallah idan ya rasu, kuma ya bi jana'izarsa har sai an binne shi.