explain-icon

Bayani

(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata aagre shi ya kasance idan zai yi atishawa: Da farko: Yana ɗora hannunsa, ko tufafinsa akan bakinsa; dan kada wani abu da zai cutar da abokin zamansa ya fita daga bakinsa ko hancinsa. Na biyu: Yana ƙanƙar da muryarsa ba ya ɗaga ta.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Bayanin shiriyarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a atishawa, da kuma koyi da shi a hakan.
  • An so (mai atishawa ya) ɗora tufafi ko hankici da makancinsa akan bakinsa da hancinsa idan zai yi atishawa, domin kada wani abinda zai cutar da abokin zamansa ya fito daga gare shi.
  • Kanƙar da murya a atishawa abin so ne, hakan yana daga cikar ladabi, da kuma kyawawan ɗabi'u.