Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana dukan mata, sai sarkin muminai Umar Ibnu Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya zo kuma ya ce: Ya Manzon Allah mata sun yi wa mazajensu tawaye kuma ɗabi'unsu sun munana. Sai (Manzon Allah) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi rangwami da dukansu dukan da ba zai sa ciwo ba idan an samu sababin yin hakan, kamar idan sun ƙi bada haƙƙin miji da kuma saɓa masa da makamancin haka. Sai wasu mata suka zo a bayansa wurin matan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suna kawo ƙara akan dukan mazajensu dukan da ba zai sa rauni ba, saboda mummunan aiki da wannan rangwamen, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Waɗannan mazajen waɗanda suke dukan matansu dukan da ba zai sa rauni ba ba zaɓɓɓunku ba ne.