explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana daya daga sabubban da suke karfafa alaka tsakanin muminai kuma suke yada soyayya a tsakaninsu, shi ne cewa idan mutum ya so dan'uwansa to ya sanar da shi cewa shi yana son sa.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Falalar tsarkakakkiyar soyayya saboda Allah - Madaukakin sarki - ba dan maslaha ta duniya ba.
  • Anso sanadar da wanda ake so sabo da Allah da soyayyrsa, dan soyayya da kauna su karu.
  • Yada soyayya tsakanin muminai yana karfafa 'yan uwantaka ta imani, kuma yana kiyaye zamantakewa daga rarrabuwa.