Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa idan musulmi ya sanya huffinsa bayan ya yi alwala, sannan ya kari (hadasi) bayan nan kuma ya yi nufin alwala, to yana da damar yin shafa akansu idan ya yi nufin hakan, kuma ya yi sallah da su kada ya ciresu a wani sanannen lokaci, sai dai idan ya samu janaba to cire huffin ya wajaba a gare shi saboda yin wanka.