explain-icon

Bayani

Huzaifa Dan Yaman - Allah Ya yarda da su - yana bada labarin cewa shi ya kasance tare da annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya so ya yi fitsari, sai ya shiga jujin wasu mutane; shi ne gurin da ake zubar da tsummokara da sharar da ake sharewa a cikin gidaje, sai ya yi fitsari alhali shi yana tsaye, ya kasance mafi yawancin al'adarsa shi ne ya yi fitsari a zaune. Sai Huzaifa ya yi nesa da shi, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce masa: Ka kusanto, sai Huzaifa ya kusanto gare shi har ya tsaya a bayansa daura da ƙarshen diga-digansa; dan ya zama kamar kariya gare shi daga kallonsa a wannan halin. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi alwala, lokacin wanke ƙafafuwansa biyu, sai ya wadatu da shafa akan kuffinsa biyu - su ne abinda ake ɗaurawa a ƙafa na fata mara kauri da makamancinta kuma yana zama mai suturce idan sawu - kuma bai ciresu ba.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Halaccin shafa akan kuffi biyu.
  • Halaccin yin fitsari a tsaye da sharaɗin kada wani fitsarin ya same shi.
  • Yadda annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agre shi - ya nemi juji, shi ne bola da shara domin cewa su a galibi masu sauƙi ne fitsari ba zai dawowa mai yin fitsarin ba.