explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nema daga baffansa Abu Dalib alhali shi yana magagin mutuwa da ya furta; Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, dan ya cece shi da ita ranar Alkiyama , kuma ya yi masa shaidar Musulunci, sai yaki furta shaidar dan tsoron kada Kuraishawa ta zargeshi ta ce da shi: Cewa shi ya musulunta ne saboda tsoron mutuwa da rauni! sai ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi: Da badan haka ba da na shigar da farin ciki a zuciyarka da furta shaidar, na isar da burinka har ka yarda! sai Allah Ya saukar da ayar da take nuni akan cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba ya mallakar shiriya ta dacewa da Musulunci, kawai Allah - Mai girma da daukaka -Shi kadai ne Yake datar da wanda Yake so. Kuma Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi -yana shiryar da halitta ta shiryarwa da bayani da kira zuwa hanya madaidaiciya.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Ba'a barin gaskiya dan tsoro daga zancen mutane.
  • Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kadai yana mallakar shiriyar nuni ne da fadakarwa kawai ba shiriyar dacewa ba.
  • Halaccin ziyarar kafiri mara lafiya dan kiransa zuwa ga Musulunci.
  • Kwadayin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan kira zuwa ga Allah - Madaukakin sarki - a kowane hali.