Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da Abdullahi Ibnu Jud'an, ya kasance yana daga shugabannin Kuraishawa kafin Musulunci, Yana daga kyawawan ayyukansa cewa shi: Yana sada zumuncin 'yan uawansa, yana ciyar da miskinai, da wasunsu daga cikin mafifitan ayyukan da Musulunci ya kwadaitar akan aikatasu, da cewa wadannan ayyukan ba za su anfanar da shi a lahirarsa ba; saboda kafircewarsa ga Allah, kuma shi bai taba fada ba ko sau daya: Ya Ubangiji ka gafarta mini kuskurena ranar sakamako.