Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah Ya umarce shi da yakar mushrikai har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai ba Shi da abokin tarayya, kuma su shaida manzanci ga (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da aiki da abinda wannan shaidar ta hukunta na kiyayewa akan salloli biyar a yini da dare, kuma su bada zakka ta wajibi ga wadanda suka cancanta. Idan suka aikata wadannan al'amuran to Musulunci ya tsare jinanensu da dukiyoyinsu, kashe su ba ya halatta sai dai idan sun aikata laifi ko wata barnar da za su cancanci kisa akanta, ta hanyar wajabcin hukunce-hukuncen Musulunci, sannan ranar AlKiyama Allah - Madaukakin sarki - Zai jibinci hisabunsu inda Yake sanin sirrikansu.