Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗar da musulmi ya ce wa ɗan'uwansa musulmi: Ya kai kafiri, to haƙiƙa ɗayansu ya cancanci kalmar kafircin, idan ya kasance kamar yadda ya faɗa ne, inba haka ba kafirtawar da ya yi wa ɗan'uwansa za ta dawowa wanda ya fada.