Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa ayyuka nau'uka shida ne, kuma mutane sinfi hudu ne. Ayyuka shidan su ne: Na farko: Wanda ya mutu alhali shi ba ya tarayya da wani abu ga Allah to Aljanna ta tabbata a gare shi. Na biyu: Wanda ya mutu alhali shi yana taranya wani abu da Allah wuta ta tabbata a gare shi yana madawwami a cikinta. Su ne tabbatattu guda biyu. Na uku: Kyakkyawa da aka niyyata, wanda ya yi niyyar aikata kyakkyawa kuma ya kasance mai gaskiya a cikin niyyarsa har sai ya jiyar da zuciyarsa hakan, kuma Allah Yana sanin wannan niyyar daga gare shi, sannan wani al'amari ya bijiro gareshi ba zai iya aikata wannan kyakkyawan ba za'a rubuta masa kyakkyawa cikakkiya. Na hudu: Mummuna da aka aikata. wanda ya aikata wata mummuna za'a rubuta masa mummuna daya. Su biyun: Tamka da tamka ne ba tare da ribanyawa ba. Na biyar: Kyakkyawar da take da goma irinta, ita ce wanda ya yi niyyar aikata kyakkyawa ya kuma aikatata; za'a rubuta masa kyakkyawa goma. Na shida: Kyakkyawar da take kasancewa da kaykkyawa dari bakwai, ita ce wanda ya ciyar da wata ciyarwa daya a tafarkin Allah sai a rubuta masa wannan kyakkyawar da kyakkyawa dari bakwai, wannan daga falalarSa ne - tsarki ya tabbara maSa Ya daukaka - da karamcinSa ga bayinSa. Amma sinfin mutane hudu, su ne: Na farko: Wanda aka yalwatawa a duniya daga arziki, aka ni'imtar da shi a cikinta yana samun abinda yake so a cikinta, saidai cewa shi abin kuntatawa ne a lahira kuma makomarsa ita ce wuta, shi ne kafiri mawadaci. Na biyu: Wanda aka kuntatawa a duniya daga arziki, saidai cewa abin yalwatawa ne a lahira, kuma makomarsa ita ce Aljanna, wannan shi ne mmumini talaka. Na uku: Wanda aka kuntatatawa a duniya da lahira, shi ne kafiri talaka. Na hudu: Wanda aka yalwatawa a duniya da lahira, shi ne mumini mawadaci.