Wasu daga talakawa cikin sahabbai sun kawo kukan halinsu da talaucinsu ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da rashin sadakarsu da dukiyoyi dan su samu lada mai yawa kamar yadda 'yan uwansu masu dukiya da yawa suka samu kuma dan su aikata alheri kamar su; inda cewa su (masu Hali) suna yin sallah kamar yadda muke yin sallah, kuma suna azimi kamar yadda muke yin azimi, kuma suna yin sadaka da ragowar dukiyoyinsu, mu kuma ba ma yin sadaka! Sa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da su akan abinda suke da iko akansa na sadakoki, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Shin yanzu Allah Bai zamo Ya sanya muku abinda zaku dinga sadaka da shi ba akan kanku?! domin cewa faɗinku: Subhanallah, (Tsarki ya tabbata ga Allah) zai zama ladan sadaka gareku, haka nan faɗin: Allahu Akbar, (Allah ne Mafi girma) sadaka ne, da faɗin: La’ilaha illallahu, (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah) sadaka ne, da (Horo da aikin alheri) sadaka ne, da (Hani daga abin ƙi) sadaka ne, kai a cikin jima'in ɗayanku ma ga matarsa sadaka ne. Sai suka yi mamaki, suka ce: Ya Manzon Allah, shin ɗayanmu zai zo wa sha'awarsa kuma ya zama a cikinta akwai lada?! Ya ce; Shin kuna ganin da ace ya sanyata a cikin haram na zina ko waninsa shin zai zama akansa akwai zunubi? to haka nan idan ya sanyata a cikin halal zai zama yana da lada.