Dan Mas’ud Allah Ya yarda da shi, yana ba da labarin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya koya musu huɗubar buƙata, wato wadda ake faɗa lokacin buɗe magana a huɗubobi, da kuma kafin faɗin buƙatar mai jawabi, kamar huɗubar aure da huɗubar Juma’a da sauransu. Wannan huɗubar ta ƙunshi ma’anoni masu girman gaske na bayanin cacncantar Allah ga dukkanin nau’o'in yabo, da neman taimakonSa Shi kaɗai ba shi da abokin tarayya, da neman yafiyar zunubai da kankarewsu , da neman kariyarSa daga dukkan sharri, da sharrin kai da sauransu. Sannan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ba da bayanin, ita shiriya tana hannun Allah ne, wanda kuma Ya shiryar da shi, to, babu mai ɓatar da shi, wanda kuma ya ɓatar, to, babu mai shiryar da shi. Sannan ya ambaci shaidawa da Tauhidi, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, da shaidawa da Manzanci da cewa Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) bawanSa ne kuma manzanSa ne. Sai Kuma ya rufe wannan huɗubar da ayoyi guda uku waɗanda suka ƙunshi umarni da jin tsoron Allah maɗaukaki ta hanyar aikata umarninSa da kuma nisantar abin da Ya hana don neman yardar Allah, kuma sakamakon wanda ya aikata haka kyautatuwan ayyuka da maganganu da kankarewar zunubi da gafarta laifuka, da kuma kyakyawar rayuwa a duniya, da rabauta da aljanna ranar Alƙiyama.