Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga wurin baffansa Abu Dalib alhali shi yana kan gargara, sai ya ce masa: Ya baffana, ka ce : "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, wata kalmace da zan yi maka shaida da ita a wurin Allah, sai Abu Jahal da Abdullahi Dan Abu Umayya suka ce: Ya Abu Dalib, zaka bar tafarkin babanka Abdul Muddalib?! Shi ne bautar gumaka, basu gushe ba suna yi masa magana har ya fadi karshen wani abinda ya zantar da su da shi: Akan tafarkin Abdul Muddalib, tafarkin shirka da bautar gumaka, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Zan roka maka gafara muddin Ubangijina bai hanani hakan ba, sai fadin Allah - Madaukakin sarki - ya sauka: {Bã ya kasancẽwa ga Annabi da waɗanda suka yi ĩmãni, su yi istigifãri ga mushirikai, kuma kõ dã sun kasance ma'abũta zumunta ne daga bãyan sun bayyana a gare su, cẽwa lalle ne, sũ, 'yan Jahĩm ne} [Al-Taubah: 113], kuma fadin Allah - Madaukakin sarki - ya sauka a sha'anin Abu Dalib: {Lalle ne kai bã ka shiryar da wanda ka so, amma kuma Allah Yanã shiryar da wanda Yake so, kuma Shi ne Mafi sani daga mãsu shiryuwa} [Al-kasas: 56], lallai cewa kai ba ka shiryar da wanda ka so shiriyarsa, kawai kai isarwa ce taka, Allah Yana shiryar da wanda yake so.