Usman al-Shahham da Farƙad al-Sabakhi sun tambayi Muslim ɗan babban sahabi Abu Bakrata - Allah Ya yarda da shi -: Shin ya ji wani hadisi daga babansa daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da fitintinu da yaƙin da zai afku tsakanin musulmai? sai ya ce: Eh, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa za'a samu wasu fitintinu bayan mutuwarsa, kuma waɗannan fitintinun wanda ke zaune babu ruwansa da su ya fi wanda ke tafiya a cikinsu alhali shi ba ya nemansu, yana bincike game da su, mai tafiya a cikinsu ya fi mai gaggawa zuwa garesu yana ta bincike game da su kuma yana tarayya a cikinsu. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da wanda fitina ta sauka ko ta faru a cikin zamaninsa kuma a wurinsa in ya samu wata mafakar da zai fake gare ta; wanda yake da raƙuman da yake kiwo to ya riski raƙumansa, wanda yake da tumakan da yake kiwo to ya riski tumakansa, wanda yake da wata ƙasa da gona to ya risku da ƙasarsa. Sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah shin kana ganin wanda ba shi da makoma fa na raƙuma ko tumakai ko ƙasa? Ya ce: Ya nufi makaminsa sai ya dandaƙa shi ya kamata shi, sannan ya gudu ya tsiratar da kansa da 'ya'yansa idan ya samu ikon tsira. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya shaidar sau uku sai ya ce: Ya Allah shin na isar? ya Allah shin na isar? ya Allah shin na isar? Sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah shin kana ganin idan an tilastani in yi tarayya tare da ɗaya daga sahu biyun, ko ɗaya daga cikin jama'a biyun, sai wani mutum ya dakeni da takobinsa, ko wata kibiya ta zo ta kasheni fa? Ya ce: Zai koma da zunubin kansa da kuma zunubin wanda ya yi kisan, kuma ranar lahira ya zama daga 'yan wuta.