explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya riƙi alƙawari daga sahabbansa wajen jagorantuwa (biyayya) ga majiɓinta al'amura da shugabanni a halin sauƙi da wahala, da halin wadata da talauci, kuma duk ɗaya ne umarninsu ya kasance daga abin da rai yake so ne ko yake ƙi, kai ko da shugabanni sun yi babakere da dukiyar jama'a ko muƙamai ko wanin hakan a kan talakawa; to, dole ne a ji [maganarsu] a yi biyayya bisa sanannun abubuwa, kada a yi musu tawaye, domin fitina da ɓarna wajen yaƙarsu ita ce mafi girma, kuma mafi tsanani daga ɓarnar da za ta faru saboda zaluncinsu, yana daga abin da suka yi alkawari a kansa cewa za su faɗi gaskiya a kowanne wuri suna masu yi wa Allah ikhlasi cikin haka, ba sa jin tsoron wanda zai zargesu.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • [Kyakkyawan] sakamakon ji da bi ga majiɓinta al'amura shi ne haɗuwar kan musulmai da watsar da rarrabuwa.
  • Wajabcin ji da bi ga majiɓinta al'amura in ba a saɓon Allah ba ne a cikin sauƙi da tsanani, da farin ciki da baƙin ciki da babakeren da za su yi.
  • Wajabcin faɗin gaskiya a duk inda muke, ba tare da mun ji tsoron zargin mai zargi ba cikin [al'amarin] Allah