Annabi ya hana tambayar Mulki; domin duk wanda ya nema kuma aka bashi to sai ya tozarta kuma sai anbarshi da kwadayinsa a cikin Duniya kuma sai ya fifita Mulkin akan lahirarsa, kuma idan aka bashi mulikin bashi ya nema ba to Allah zai taimake shi akai, kuma cewa rantsuwa akan wani abu bata hana yin Alkairi, sabida idan wanda ya rantse yaga wani Alkairin da yafi rantsuwarsa to sai ya warware rantsuwar tasa da kaffara, sannan ya aikata Alkairinsa.