Abu Musa Al’Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa shi ya zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a tare da shi akwai wasu jama'a daga kabilarsa, manufarsu ita ce Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya basu rakuman da zasu hau; dan samun damar fita yaki, sai tsira da aminci su tabbata agare shi ya yi rantsuwar cewa ba zai dauki nauyin su ba, ba shi da abinda zai dauki nauyinsu da shi, sai suka koma suka zauna tsawon wani lokaci, sannan wasu rakuma uku suka zo wa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, sai ya aika musu, sai sashinsu ya cewa sashi: Allah ba zai yi mana albarka a wadannan rakuma ukun ba; domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rantsuwar cewa ba zai dauki nauyinmu ba, sai suka zo masa suka tambaye shi , sai tsira da aminci su tabbata agare shi ya ce: Wanda ya dauki nauyinku Shi ne Allah - Madaukkain sarki -; domin cewa Shi ne Mai datarwa kuma Mai azirtawa, kadai ni sababi ne wanda hakan ya gudana ta hannuna, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai ni na rantse da Allah, idan Allah Ya so ba na rantsuwa akan wani abu da aikata shi ko na bar shi, kuma in ga wanin wannan abinda na rantse akansa shi ne mafi alheri, sai na aikata abinda yafin kuma in bar wanda na rantse akansa din, kuma in yi kaffarar rantsuwa ta.