Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa musulmai idan suka haɗu a kan shugabancin mutum ɗaya, da jama'a ɗaya, sannan wani ya zo yana son ya yi jayayya da shi a shugabanci, ko yana son raba musulmai sama da kungiya ɗaya, to, ya wajaba su hana shi da kuma yaƙarsa; don tunkuɗe sharrinsa da kuma kare jinanen musulmai.