Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa za'a shugabantar da wasu shugabanni akanmu, zamu san wasu daga ayyukansu; dan dacewarsu da abinda aka sani na shari'a, kuma zamu yi inkarin wasu ayyukan na su; dan sabawarsu ga hakan, Wanda ya ki da zuciyarsa amma ba shi da iko akan inkari; to hakika ya kubuta daga zunubi da kuma munafunci, Wanda ya samu iko akan inkari da hannu ko da harshe sai ya yi inkarin hakan akansu to hakika ya kubuta daga sabo da kuma tarayya a cikinsu, sai dai wanda ya yarda da aikinsu ya kuma bi su akansa zai halaka kamar yadda suka halaka. Sannan suka tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Shin ba ba ma yaki shugabannin da wannan ita ce siffarsu ba? mu hanasu hakan, sai ya ce: A'a, muddin dai sun tsaida sallah a cikinku.