Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bada labari game da al'amura biyu idan musulmi ya lazimce su to cewa shi zai shiga aljanna, Na farko: Kiyaye harshe daga maganar da zata fusatar da Allah - Madaukakin sarki -. Na biyu: Kiyaye farji daga afkawa a cikin alfasha. Domin cewa wadannan gabubuwa biyun afkawa cikin sabo da su yana yawaita.