Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci cewa mai kira zai kira 'yan aljanna alhali su suna cikinta suna ni'imtuwa: Lallai cewa ku zaku samu lafiya ba zaku yi masassara a cikin aljanna ba har abada duk yadda ƙarancin masassarar take, kuma cewa ku zaku rayu ba zaku mutu a cikinta ba har abada koda ya kasance bacci ne wanda shi ne mutuwa ƙarama, kuma cewa ku zaku zama samari a cikinta ba zaku tsufa a cikinta ba har abada, kuma cewa ku zaku ni'imtu ba zaku yi baƙin ciki ba ko ku yanke ƙauna a cikinta ba har abada, hakan (shi ne) faɗinSa - Mai girma da ɗaukaka -: {Sai a yi kira cewa wancananku aljanna an gadar muku ita saboda a binda kuka kasance kuna aikatawa} [al-A'araf: 43].