Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa idan musulmi ya yi sallah a cikin jama'a, sallarsa ta kasance tafi sallarsa a gidansa ko kasuwarsa sau ashirin da wani abu. Sannan ya ambaci dalili a hakan: Shi ne cewa mutum idan ya yi alwala sai ya cika alwala ya kyautatata, sannan ya tafi masallaci babu abinda ya fitar da shi sai nufin sallah, ba zai yi wani taku ba sai an daukaka matsayinsa da darajarsa da shi, kuma an shafe masa kuskure da shi, idan ya shiga masallaci ya zauna yana sauraron sallah, to shi yana samun ladan sallah da sakamakonta muddin dai ya jira sallah, Mala'iku suna masa addu'a muddin dai yana mazauninsa wanda ya yi sallah a cikinsa, suna cewa: "Ya Allah Ka gafarta masa, Ya Allah Ka karbi tubansa" muddin dai bai bata alwalarsa ba, ko ya aikata abinda mutane zasu cutu da shi ko Mala'iku ba.