explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana wanda yake cikin masallaci ya fara yin sallar nafila bayan an yi iƙamar sallar farilla.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Hani daga yin sallar nafila idan an yi iƙamar sallar farilla alhali shi yana cikin masallaci.
  • Hani akan fara nafila bayan an yi iƙamar sallah, daidai ne ta kasance ratiba ce kamar sunnar Asuba da Azahar ko waninta.
  • Idan an yi iƙamar sallah alhali shi yana yin nafila; idan mafi ƙaranci daga raka'a ya rage to ya cikata a sauƙaƙe, inba haka ba to sai ya yanketa har ya riski falalar kabbarar harama.