Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana wanda ya ci tafarnuwa ko albasa zuwa masallaci, dan kada ya cutar da 'yan uwansa daga waɗanda suka halarci sallar jam’i da warinsu, shi hanine na tsarkakewa daga zuwa masallaci, ba dan an hana cinsu ba: domin cewa su suna daga abubuwan da aka halatta, haƙiƙa an zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wata tukunya a cikinta akwai korren abubuwa, lokacin da ya shaƙi wari a cikinta kuma aka ba shi labarin abinda ke cikinta sai ya hanu daga cinta ya kuma kusantar da ita ga wani daga sahabbansa dan ya ci daga gareta, sai ya kyamaci ci dan koyi da shi, lokacin da tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya gan shi ya ce: Ka ci; domin cewa ni ina ganawa da Mala’iku idan sun zo da wahayi. kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mala'iku suna cutuwa daga warin da ake ƙi, kamar yadda mutane suke cutuwa daga gare shi.