Wani mutum makaho ya zo wurin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ya Ma’aikin Allah ! Ba ni da wanda zai taimaka min ya riƙe hannuna zuwa Masallaci a salloli biyar, yana son Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi masa rangwamen sallar jam’i, sai ya yi masa rangwamen, lokacin da ya juya ya tafi, sai ya kira shi, ya ce; Shin kana jin kiran Sallah? Ya ce; Eh, ya ce: Ka amsawa mai kiran Sallah.