Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa lada da sakamakon sallar mutum a cikin jama'a tare da liman ya fi sallah ashirin da biyar da mutum zai sallace su shi kaɗai a cikin gidansa ko kasuwarsa, sannan (annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci cewa mala'ikun dare da rana suna taruwa a sallar Asuba, sannan Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce yana mai kafa hujja akan hakan: Idan kun so ku karanta: {Lallai karatun alfijir (sallar Asuba) ya kasance abin halartar (mala'iku) ne} [al-Isra'a: 78]. Wato: Lallai sallar Asuba mala'ikun dare da mala'ikun rana suna halartarta.