explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa wanda ya zo masallaci dan yin ibada ko ilimi ko wanin hakan daga manufofin alheri a kowanne lokaci albishir; a farkon yini ko ƙarshensa da cewa Allah haƙiƙa ya tanadar masa da wani wuri da garar baƙi a cikin aljanna, duk lokacin da ya zo masallaci a dare ko yini.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Falalar tafiya zuwa masallaci, da kwaɗaitarwa akan kiyayewa akan yin sallar jam'i a cikinsa, da yawa mai ƙin zuwa masallaci alheri da falala da lada da garar baƙi suke wuce shi waɗanda Allah - alherinSa ya yawaita Ya ɗaukaka - ga masu nufin ɗakinSa.
  • Idan mutane sun kasance suna girmama wanda ya zo gidajensu, suna gabato masa da abinci, to Allah - alherinSa ya yawaita Ya ɗaukaka - Shi ne Mafi kyauta daga halittarSa! wanda ya nufi ɗakinSa zai girmama shi, kuma Allah Zai tanadar masa da masauki mai girma kuma babba.
  • Farin ciki da nishaɗi da tafiya masallatai; domin ana tanadar masa da masauki a duk lokacin ya wayi gari ko ya kai maraice da adadin tafiyarsa.