Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi sallar Asuba wata rana, sannan ya yi tambaya: Shin wane ya zo wannan sallar da muka yi? Sahabbai suka ce: A'a. Sannan ya ce: Shin wane ya zo ne? ga wani mutumin daban, Suka ce: A'a. (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Lallai sallar Asuba da Issha'i sune mafi nauyin salloli akan munafukai; dan rinjayar kasala a cikinsu, da kuma ƙarancin faruwar riya garesu, tunda ba'a ganinsu a cikin duhu. Da kun san yaku muminai abinda ke cikin sallolin Asuba da Issha'i na lada da sakamako mai ƙaruwa - domin lada yana kan gwargwadan wahala - da kun zo su koda da jan ciki ne da tafiya akan hannaye da gwiwowi. Kuma masu sahu na farko a kusancinsu da liman kamar sahun mala'iku ne a kusancinsu ga Allah - Maɗaukakin sarki -, da muminai suna sanin abinda ke cikin falalar sahun farko da sun yi tsere gare shi . Kuma lallai sallar namiji tare da namiji ita ce mafi girman sakamako da tasiri a sallarsa shi kaɗai, kuma sallarsa tare da maza biyu tafi tare da namiji ɗaya, Sallar da masallatan suka yi yawa a cikinta ita ce mafi soyuwa ga Allah kuma ta fi lada.