Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya kasance a zaune tsakanin sahabbansa, sai ya ce:: Wannan lokacin da za'a dauke a zare ilimi ne daga mutane. Sai Ziyad Dan Labid Al-Ansary - Allah Ya yarda da shi - ya yi mamaki kuma ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, Sai ya ce; Ta yaya za'a dauke ilimi a sarayar da shi daga garemu?! Alhali mun karanta Alkur’ani mun haddaceshi; na rantse da Allah sai mun karantashi, kuma mun karantar da matanmu da 'ya'yanmu shi, da 'ya'yan 'ya'yanmu, Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce yana mai mamaki: Mahaifiyarka ta rasaka ya Ziyad! na kasance ina lissafaka daga malaman mutanen Madina! Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana masa: Cewa rasa ilimi bai zamo da rasa Alkur’ani ba; saidai rasa ilimi (yana kasancewa ne) da rashin aiki da shi, Wannan Attaurar da Injilar dake wajen Yahudawa da Nasara; a tare da haka ba ta anfanesu ba, kuma ba su anfana da manufarsu ba; shi ne aiki da abinda suka sani.