Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa daga alamomin kusantowar tashin Alkiyama dauke ilimi na shari'a, wannan kuwa ta hanyar mutuwar malamai ne. Sakamakon hakan jahilci zai yawaita ya yadu, zina da alfasha zasu yadu, shan giya zai yawaita, adadin maza zai karanta , adadin mata zai karu; har yakasance namiji daya zai tsayawa mata hamsin ga al'amuransu kuma zai jibinci maslahohinsu.