Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana rantsuwa akan kusancin saukar (Annabi) Isa dan Nana Maryam - aminci ya tabbata agare shi - dan ya yi hukunci a tsakanin mutane da adalci da shari'ar Annabi muhammadu, kuma shi zai karya gicciyayye (kros) wanda kiristoci suke girmama shi, kuma Annabi Isa - aminci ya tabbata agare shi - zai kashe alade, kuma cewa shi aminci ya tabbata agare shi zai sarayar da jiziya zai dora mutane gaba dayansu a shiga Addinin Musulunci. Kuma dukiya za ta yawaita wani ba zai karbeta ba; dan yawanta, da wadatuwar kowa da abinda ke hannunsa, da saukar albarka da malalowar alkairai.