Za'a tambayi mumini a cikin ƙabari, sai mala'iku biyu waɗanda aka wakilta da hakan su tambaye shi su ne Munkar da Nakir, kamar yadda ambatansu ya zo a Hadisai masu yawa, sai ya shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah , kuma cewa (Annabi) Muhammad manzon Allah ne, Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: wannan shi ne tabbatacciyar magana wacce Allah Ya faɗa a cikinta: {Allah Yana tabbatar da wadanda su ka yi imani da magana matabbaciya a rayuwar duniya da kuma a lahira} [Ibrahim: 27].