Wasu tsoffin Mata guda biyu daga cikin tsoffin Yahudawan Madina sun shigo mun, sai suka ce da ni:Lallai Na Qabari ana yi musu Azaba a cikin Qabarinsu, sai na qaryatasu, kuma ban so na gasgata su ba, sai suka futa, kuma Manzon Allah SAW ya shigo sai na ce da shi: ya Manzon Allah, Wasu tsoffin Mata biyu kuma na gaya masa labarin, sai ya ce:"Sunyi Gaskiya, lallai su ana yi musu Azaba Azabar da Dabbobi suke ji baki xayansu" kuma ban tava ganinsa a wat a sallah ba face sai ya nemi tsari daga Azabar Qabarin