Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya bada labarin cewa Alkiyama ba za ta tsaya ba har sai mutum ya wuce kabari, sai ya yi burin ya zama matacce a bigirensa, sababi shi ne tsoronsa akan kansa na tafiyar Addininsa saboda rinjayar karya da ma'abotanta, da bayyanar fitintinu da sabo da abubuwan ki.