Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa daga alamomin Alkiyama manya; shi ne bullowar rana daga yamma maimakon daga gabas, lokacin da mutane suka ganta za su yi imani gaba daya, A wannan lokacin imanin kafiri ba zai anfanar da shi ba, kuma aiki na gari ba zai yi amfani ba haka kuma tuba. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Alkiyama zata zo kwatsam; har cewa ita zata tashi alhali mutane suna cikin harkokin su da kuma sha'aninninkan rayuwarsu; Sai Alkiyama ta tashi alhali mai siyarwa da mai saya sun shimfida tufafinsu a tsakakninsu, amma ba za su saida su ba, ba kuma za su ninke su ba. Kuma Alkiyama zata tashi alhali hakika mutum ya dauki nonon taguwarsa mai yawan nono amma ba zai sha shi ba, Alkiyama za ta tashi alhali mutum yana gyara tafkinsa yana tsaftace shi amma ba zai shayar a cikinsa ba, Alkiyama za ta tashi alhali mutum ya daga lomarsa zuwa bakinsa dan ya ci amma ba zai ci ba.