explain-icon

Bayani

Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - yana bada labarin cewa: An saukar da wahayi ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma an aiko shi alhali shekarunsa arba'in, sai ya zauna a Makka shekara goma sha uku bayan wahayi, sannan aka umarce shi da hijira zuwa Madina, ya zauna a cikinta shekara goma, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya rasu shekarunsa sittin da uku.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Himmatuwar sahabbai da tarihin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.