Annbai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah Ya ba shi wasu dabi'u uku (wadanda) bai bada su ga wani daga Annabwa a gabnina ba. Na farko: An bani nasara da tsoro da za'a jefa shi a cikin zukatan maƙiyana koda tsakanina da su akwai tafiyar wata. Na biyu: An sanya mana ƙasa ta zama masallacin da zamu dinga sallah a duk inda muke, kuma mai tsarkakewa da turɓaya a yayin rasa ruwa, ko gaza anfani da shi. Na uku: An halatta mana ganimomin yaƙi, sune waɗanda musulmai suke ɗiba a yaƙoƙinsu tare da kafirai. Na huɗu: An bani ceto mafi girma dan hutar da mutane daga firgicin tsayuwa a ranar Alkiyama. Na biyar: An aikoni zuwa halitta gaba ɗaya mutanensu da Aljanunsun, saɓanin Annabawa kafin ni sun kasance ana aikosu ne zuwa mutanensu ne kawai.