explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa dukkanin al'ummarsa za su shiga aljanna sai wanda ya ƙi! Sai sahabbai - Allah Ya yarda da su - suka ce: Wa zai ƙi ya Manzon Allah?! Sai (manzon Allah) tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya amsa musu cewa: wanda ya miƙa wuya ya bi Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - zai shiga aljanna, amma wanda ya saɓa bai miƙa wuya ga shari'a ba, to, haƙiƙa ya hanu daga shiga aljanna da ayyukansa munana.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Lallai cewa bin Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana daga biyayyar Allah, kuma saɓa masa yana daga saɓawa Allah.
  • Bin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana wajabta aljanna, saɓa masa kuma yana wajabta wuta.
  • Albishir ga masu biyayya daga cikin wannan al'ummar, kuma cewa su dukkaninsu za su shiga aljanna, sai wanda ya saɓawa Allah da Manzonsa.
  • Tausayinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ga al'ummarsa, da kwaɗayinsa a kan shiriyarsu.