Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa; Allah Ya buga wani misali ga Musulunci da hanya madaidaiciya mikakkiya babu karkata a cikinta, agefan wannan hanyar akwai ganuwowi biyu, to bangwaye da suke kewaye da ita ta fuskarsa su ne iyakokin Allah, wasu budaddun kofofi suna shiga wadannan ganuwowi biyun su ne Abubuwan da Allah Ya haramta, akan wadannan kofofin akwai labulayen da basa bayyanar da wanda yake cikinsu ga mai wucewa akan hanyar, afarkon hanyar akwai wani mai kira yake fuskantar da mutane kuma yake shiryar da su yana ce musu: Ku tafi akansa ba tare da kun karkace zuwa wani bangaren ba, wannan mai kiran duk lokacin da mai tafiya akan tafarkin ya yi niyyar ya bude wani gwargwado mai sauki daga labulayen kofofin sai ya tsawatar masa ya ce da shi: Kaicanka kada ka bude shi! domin cewa kai idan ka bude shi zaka shigeshi kuma ba zaka sami damar kare kanka ba daga shiga, wannan mai kiran shi ne mai wa'azin Allah a cikin zuciyar kowane Musulmi.