Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin dayanku yana son idan ya koma zuwa iyalansa ya samu manyan taguwowi masu ciki masu giba?" muka ce: Eh. Ya ce; "To ayoyi uku dayanku zai karantasu a cikin sallarsa sun fiye masa alheri daga taguwowi uku manya masu ciki".
Ingantacce ne - Muslim ne ya rawaito shi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa ladan karanta ayoyi uku a cikin sallah; shi ne mafi alheri daga mutum ya sami taguwowi uku masu ciki manya a cikin gidansa.
Daga Cikin Fa idodin Hadisin
Bayanin falalar karanta Alkur’ani a cikin sallah.
Ayyuka na gari su ne mafi alheri kuma mafi wanzuwa daga jin dadin duniya mai karewa.
Wannan falalar ba ababen kayyadewa bane da karanta ayoyi uku kawai; duk lokacin da mai sallah ya kara karanta ayoyi a cikin sallarsa ladanta zai zama mafi alheri gare shi daga adadinsu daga taguwowi masu ciki.