Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana abubuwa hudu: Na farkonsu: Hana mace daga tafiyar kwana biyu ba tare da mijinta ba ko daya daga muharramanta ba, shi ne wanda ta haramta agare shi haramci na har'bada daga 'yan uwa, kamar Da, da uba, da Dan dan uwa da dan 'yar uwa, da baffa da kawu, da makamancin hakan. Na biyunsu: Hani daga azimin ranar ƙaramar sallah da ranar babbar sallah, duk daya ne musulmi ya azimce su ne akan bakance (alwashi) ko nafila, ko kuma kaffara. Na ukunsu: Hani daga sallar nafila bayan sallar la'asar har sai rana ta fadi, da bayan bullowar alfijir har sai rana ta bullo. Na hudunsu: Hani daga tafiya zuwa wani wuri daga wurare da ƙudirce falalarsu da ƙudirce ninkin kyawawan lada a cikinsu, in banda wadannan masallatan uku, to ba'a daure sirdi ga wasunsu dan yin sallah a cikinsu, domin lada ba'a ninkashi sai a wadannan masallatan uku: Masallaci mai alfarma (Dake Makka), da masallacin Annabi (Dake Madina), da masallacin Kudus (Dake Falasdin).